By Yusuf Mohammed Lawn, Gombe
Kansila mai wakiltan yankin Waziri TA arewa dake karamar hukumar Dukku, jihar Gombe Hon. Hauwa Saidu Muhammad, wacce aka fi sani da Hajiya Ummi ta fara cika alkawarin datayiwa jamaar yankinta yayin da tafara samar musu da nagartaccen ruwansha gami da musu bushara da samar da wutan lantarki da sauran abubuwan more rayuwa.
Hon Hauwa ta bayyana haka ne a lokacin da take kaddamar da bude ruwan fanfo a mazabarta jiya alhamis
Kansilan tayi kira ga jamaar yankinta da sucigaba da mutunta shugabanni da yin biyayya garesu. Takuma yi amfani da damar da tasamu ta mika godiya ga shugaban kamar hukumar Dukku don hadin kai da goyon baya da take samu



No comments:
Post a Comment