Friday, May 22, 2026

Gasar Kofin Duniya 2026 : FIFA Zata Fara Watsa Fassarar Harshen Kurame (Sign Language)

 

By Ability News Network

22 ga Mayu, 2026, 1:32 na rana

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA, ta sanar da cewa Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta shekarar 2026 za ta kasance karo na farko da za a rika watsa dukkan wasannin gasar tare da fassarar harshen kurame, a wani mataki na ƙara bai wa masu nakasa damar kallon wasanni cikin sauƙi.

A cewar sanarwar da aka wallafa a shafin hukumar ranar Juma’a, an ƙaddamar da wannan tsari ne domin tabbatar da cewa dukkan magoya baya, musamman masu nakasa, za su iya jin daɗin kallon wasanni ko a filin wasa ko kuma daga gida.

“FIFA ta himmatu wajen tabbatar da cewa dukkan magoya baya, ciki har da masu nakasa da iyalansu da abokansu, sun samu kyakkyawan ƙwarewa a Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta wannan shekara,” in ji FIFA.

Sabbin shirye-shiryen sauƙaƙe wa masu nakasa sun ginu ne kan ayyukan da aka fara amfani da su a Gasar Kofin Duniya ta Kungiyoyi ta FIFA ta 2025, ciki har da jakunkunan taimakon masu matsalar ji da kuma sharhin sauti ga masu matsalar gani.


Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, a shekarar 2026, FIFA za ta ƙara amfani da allunan taɓawa da kuma ƙarin ayyukan tallafi ga masu matsalar ji ko fahimta.

Babban abin da ya fi jan hankali shi ne fara watsa dukkan wasanni da fassarar harshen kurame kai tsaye. FIFA ta bayyana cewa wannan ba kawai fassarar magana ba ce, har ma da isar da cikakken yanayin wasan.

“Fassarar wasan da harshen kurame ta wuce fassarar kai tsaye kawai. Tana bai wa kurame da masu matsalar ji damar jin daɗin yanayin wasan gaba ɗaya,” in ji sanarwar.

A cewar FIFA, masu fassarar za su rika bayyana yadda wasa ke gudana tare da yanayin filin wasa, kamar busar alkalin wasa, hayaniyar magoya baya da kuma sauyin yanayin wasa.

Hukumar ta kuma bayyana tsarin harsunan kurame da za a yi amfani da su a yankuna daban-daban. Wasannin da za a buga a Amurka da Canada za su yi amfani da Harshen Kurame na Amurka (ASL), yayin da wasannin Mexico za su yi amfani da Harshen Kurame na Mexico (LSM).

A matakin wasannin fitar da gwani, za a fi amfani da ASL a mafi yawan wasanni, yayin da za a samar da LSM a wasu wasannin da ƙasashen masu amfani da Sifaniyanci za su buga.

Masoya ƙwallo za su iya samun wannan sabis ta hanyar manhajar hukuma ta Gasar Kofin Duniya, inda za su shiga sashen “Accessibility Services” sannan su kunna zaɓin “Sign Language” domin kallon watsa shirye-shiryen da aka tanada.

FIFA ta ce wannan mataki wani ɓangare ne na dogon shirin ta na tabbatar da haɗin kai da bai wa kowa dama a harkar ƙwallon ƙafa, domin gasar ta kasance mai sauƙin isa ga kowa da kowa.

No comments:

Post a Comment

Arsenal PWD Fans, Others Light Up Gombe with Glittering Trophy Parade to Celebrate Club’s Historic Premier Leaque Tittle Triumph

  _By Yusuf Mohammed Lawan| Ability News Network | Gombe_  31st May, 2026  Gombe came alive on Monday as thousands of Arsenal supporters, in...