Wednesday, September 4, 2024

Ayyukan Jinkai da Dr. Halimat tayi Kawai Sun Isa Shugaba Tinubu ya Bata Mukamin Ministar Jinkai ta Tarayya - Hon. Adnan A. Daneji

 

By Yusuf Mohammed Lawan, Sept 4th, 2024


Tsohon mai bawa Gomnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje Shawara kan harkokin masu bukata ta musamman, Hon. Adnan Ali Daneji, shaharraren dan siyasa ne kurma wanda jajiceccene wajen harkar siyasa a tattaunawar dayayi da wakilin ABILITY NEWS NETWORK (YUSUF MOHAMMED LAWAN) ya bayyana Dr. Halimat Adenike Tejuosho, CEO/Founder na cibiyar jinkai Wanda akafi sani da Queen Adenike Tejuosho QAT Foundation, a mastayin jajircecciyar mai jinkai da tafi kowa cancantar zama ministar jinkai a duk fadin Najeriya. Hon. Daneji har ila ya zakulo kadan daga cikin  kyawawan halayen Dr. Halimat Adenike Tejuosho Wanda da wuya a samu jami'in gomnati dake da irinsu a fadin Najeriya. 

Asha karatu lafiya 

ANN : Masu karatunmu zasu so sanin ko wanene Hon. A Daneji?

 Hon. Adnan Ali Daneji ba kowa bane wani bawan Allah ne haifaffen jihar kano karamar Hukumar gwale mazabar sani Mai nagge unguwar mazaunar tanko duk a jihar kano

Hon. Adnan Ali Daneji shine tsohon Mai bawa gwamna jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje shawara akan al-amuran masu bukata ta musamman.

ANN:  A takaice kawo abubuwa guda uka da Dr. Tejousho tayi wa masu bukta ta musamman  da ya faranta musu rai sosai kuma Wanda bazasu iya mantawaba a rayuyarsu

HAD: Alhamdilillahi.Farko Babu abinda zamu cewa Dr. Halimat sai Godiya tayi abubuwa fiye da 3 zan baka amsa kamar yadda ka bukata

 Dr. Halimat tana tallafawa masu bukata ta musamman da tallafin biyan kudin makaranta lokaci zuwa lokaci

Bata tsaya iya nan ba ta Raba kayan tallafin Jinkai Irinsu shinkafa, sukari, da kayan ABINCI na miliyoyin naira a lokacin azumi da bikin sallah babba da karama ga masu bukata ta musamman na babban birnin tarayya Abuja da sauran jihohin Nigeria

Kada ka manta Dr Halimat bata rike da kowanne irin mukami na gwamnati illa kawai tana taimakawa ne da aljihunta da dukiyarta daidai gwargwado

A Yan lokutan nan tsakanin jiya da yau dr Halimat ta fitar da zunzurutun kudi har sama da 2million ta rabawa sama da masu bukata ta musamman na kasar nan 100 tallafin 20,000 kowannensu domin rage musu radadin halin da alumma suke ciki

Wadannan kadan ne daga cikin ayyuakan Jinkai na Dr.Halimat  Tejuosho Ta gidauniyarta Mai Albarka wato QAT foundation

ANN:  Kamar yadda Dr. Tejousho ta jajirce dayin ayyukan jinkai a wurare daban daban, shin akwai alaka tsakanin aikace - aikacen jinkan da Dr. Tejesho ke gudanarwa da shirin Renewed Hope Agenda na shugaba Tinubu?

HAD : Tabbas Dr Halimat Adenike Tejousho tana taimakawa shirin renewed Hope Agenda na president Ahmed Bola Tinubu domin cimma burinsa na tallafawa alummar kasar nan da Kuma kawo sauyi mai Albarka bisa Imani da tayi cewa tunibu babban burinsa shine tallafawa alummar kasar nan da Kuma Kai kasar nan ga turba Mai kyau wannan shine babban abinda ya janyo Hankalin Dr. Halimat tashigo cikin shirin renewed Hope Agenda domin ta bada tata gudunmawa a matsayinta Yar kasa ta gari Mai burin ganin rayuwar alumma ta inganta

ANN: Wane halayen Dr. Tejousho suka fi burge ka da sauran masu bukata ta musamman da yasa kuke Mara mata baya ta zama ministar jinkai fiye da sauran mutane?

HAD; Babban abinda yake birge ni na halayen Dr Halimat sune kamar haka:

HAKURI: Tabbas Dr Halimat tana da hakuri da Kuma kawar da Kai tare da yafiya

TAUSAYI; Dr. Halimat tana da tausayi da son ganin alumma sun samu saukin rayuwa cikin Jin dadi da walwala ba tare da sun kuntata ba

KAWAR DA KAI; Dr Halimat tana da kawar da Kai ga duk masu nufinta da sharri hasalima bata son munafunci ko kawo mata tsegumi da gulmace gulmace 

JAJIRCEWA: Dr. Halimat  tana da jajircewa wajen tsayawa akan duk abinda ya shafi rayuwar masu bukata ta musamman da sauran alumma marasa galihu cikin ruwa da iska zata shiga domin tallafa musu ko share musu hawaye

Dr. Halimat macece Mai kamar Maza wajen Kula da bukatun alumma babba da yaro ba tare da nuna bambancin yare ko addini ba. Wadannan sune kadan DAGA CIKIN halayen Dr Halimat

ANN :Ma'aikatar jinkai da rage fatara ta tarayya tana bukatan shugabanci mai kyau fiye da sauran ma'akatun kasa saboda muhimmancin abubuwan  da aka kayyade don tafiyar da harkokin jin dadin rayuwa da walwalar al-umma. Kana ganin Idan shugaba Tinubu zai nada ministar dazata cigaba da kulawa da aiyukan jin dadi, wakake ganin yakamata shugaba Tinubu ya zaba, kuma menene hujjarka?

HAD: Alhamdilillahi. Tambaya Mai muhimmanci kenan- Hausawa suka ce tun daga laraba ake Gane alherin Juma'a

Hakika Dr Halimat daya ce tankar dubu a cikin duk ministocin da suke cabinet din Tinubu 

Kasancewarta gogaggiya a fannin Jinkai data shahara wajen tallafawa alumma marasa galihu tsawon  lokacin data dauka ba tare da sisin kwabon gwamnati ba wannan wata babbar Yar manuniya ce ta nuna tabbas zata bawa mara da kunya wajen fitar da miliyoyin alumma musamman matasa da marasa galihu, uwa uba masu bukata ta musamman daga kangin talauci da matsalolin rashin aikinyi da dogaro da Kai wajen bawa matasa damar cigaba da cin gajiyar tsarin Npower karkashin Renewed Hope Agenda na shugaba kasa 

Hakika Dr Halimat Adenike Tejuosho wacce ake mata lakabi da Garkuwar  marayu Kuma uwa ga masu bukata ta musamman na kasar nan itace daya tilo daya kamata Mai girma shugaban kasa ya nada a matsayin minitsan Jinkai na tarayyar Nigeria ba tare da bata lokaci ba lura da tsarinta na son tallafawa alumma fiye da wasu nadaddun ministocin. 

ANN: A dai-dai  wannan lokaci da yan Najeriya ke bukatar shugabanci nagari ruwa a jallo, musamman a ma'aikatar jinkai ta tarayya wacce ke fuskantar barazanar almundahana da dukiyar al'umma, wace shawara zaka bawa mahukunta a mastayinka na shahararren dan siyasa?

HAD: Babban shawarata ga duk masu rike da madafun Iko shine su Saka gaskiya da rikon amana a shaanin mulki da cigaban kasa ta yadda Yan kasar nan zasu gamsu tabbas ana mulkin adalci.

 Wajibi ne su hada Kai wajen yakar rashawa da kashe kudaden Yan kasa ba bisa kaida ba muddin suka tsaya suka nazari a bangaren tattalin arziki da taka tsantsan abubuwa zasu tafi daidai da kyautatawa muradun Yan kasa bisa Doron adalci da tsarin mulki da Yancin Dan Adam Kamar yadda tsofaffin shugabanni yan mazan jiya suka shinfida mulki na adalci da kyautatawa yan kasa. 

Su fito da tsare tsaren kimiyya da fasaha da hadin Kan kwararru a matakin farko domin dakile matsalolin da ake fuskanta na arzikin  kasa da wahalhalun da alumma suke fuskanta bisa yadda masu rike da mukamai na gwamnati suke tafiya ba akan turba ba

A tsarin Jinkai da kaucewa almundahana kamar yadda na bada shawara cewa muddin aka nada Dr. Halimat Adenike Tejuosho a matsayin minitsan Jinkai to tabbas duk wata almundahana zata zama tarihi a maaikatar Jinkai bisa kyawawan manufofinta na Alheri da tarihinta na rikon Amana da jinkan bayin Allah da sauran alumma ba tare da nuna wariya, yare, kabila ko addini ba.

ANN: Mun code maka Hon.

HAD; Nima na gode sosai


No comments:

Post a Comment

RAMADAN: Gov. Inuwa Yahaya Distributes Food Palliatives to PWDs in Gombe

Gombe State Governor, His Excellency Alh. Muhammadu Inuwa Yahaya (Dan Majen Gombe) has distributed large quantity of food palliatives to per...